DABARUN TSARO A GARIN FADAR CHAWAI DA KE ƘARAMAR HUKUMAR KAURU, TA JIHAR KADUNA
Abstract
SHAFIN GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (SWT), Ubangijin Taliƙai mai kowa mai komai. Tsira da amincin Allah su Ƙara tabbata ga fiyayyen halitta shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W), tare da iyalan gidansa da sahabbansa da kuma waɗanda suka bi bayansa da kyawawan ayyuka na ƙwarai. Ina miƙa katafariyar godiya ga jagoran wannan aiki, watau Malam Aliyu Muhammad, wanda shi ne ya sha ɗawainiya wajen kulawa da wannan aiki da naka gabatar, Allah ya saka masa da alkhairi, Allah ya ƙara masa ɗaukaka da kariya da kuma nisan kwana. Bayan haka, ina miƙa godiya ga mahaifiyata Malama Halimatu Zakari da ta ɗauki ɗawainiya da ni tun daga haihuwata har zuwa yanzu. Ina ƙara miƙa godiya ga malamaina waɗanda suka sha fama wajen koyar da ni a Sashen Nazarin Harsuna Najeriya da Kimiyyarsu ta Jami'ar Sa'adu Zungur ta Jahar Bauchi, da ke Gaɗau. Irin su: Dr. Furera Adamu Garba (Shugaban wannan Sashe mai albarka) da Dr. Jamilu Abdullahi da Prof. Abdulmumini Isah da Malam Aliyu Muhammad da Malam Bappah Babangida da Malam Biniya Madaki da Malama Hauwa da sauran malamai waɗanda ban ambaci sunansu ba. Haka kuma ina miƙa godiya ga dukkanin iyaye da 'yan uwa da abokaina na Makaranta irin su: Abdulhameed Hudu Madaki, Ali Kabir, Musa Dantala da sauran waɗanda ban kira sunayensu ba. Ina ƙara miƙa godiyata ga abokaina na gida irin su: Abubakar Yunusa (Attajiri) da Bashar Musa da sauran waɗanda ban kira sunayen su ba. Allah ya saka musu da alkhari, domin sun ba ni gudummawa da shawarwari wajen ganin cewa na kammala karatuna lafiya ina godiya.
Full-Text Access Notice
In accordance with the NERD Policy on promoting peer-reviewed publication, public access to the full text of a project, thesis or dissertation is restricted for three years, allowing the author and supervisors sufficient time to pursue peer-reviewed publication.
During this period, researchers with legitimate academic or research purposes may request authorisation directly from the author to enable NERD to release the indexed full texts of the work using the form below.